1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren neman juyin juya hali a Angola

September 18, 2013

Matasan Angola sun shirya gudanar da wata zanga-zangar kin jinin gwamnatin a ranar Alhamis, duk da cewa suna yia cin karo da fushin hukumomin tsaron kasar.

https://p.dw.com/p/19kIT
epa03375485 Members of the Patriotic Youth of Angola protest against irregularities in the election process, close to the National Election Commission, in Luanda, Angola, 30 August 2012. Angola will hold general elections on 31 August, which will define the composition of Parliament and who will be the President and Vice President of the Republic. Incumbent President Jose Dos Santos, who has been in power since 10 September 1979, is expected to win by a large margin. EPA/PAULO NOVAIS +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Wata kungiyar matasa a kasar Angola ta shirya gudanar da wani jerin gwano ranar Alhamis a Luanda babban birnin kasar don nuna adawa da mulkin kama karya na gwamnatin shugaba Jose Eduardo dos Santos, duk da fargabar cewa 'yan sanda ka iya daukar matakan murkushe su. Kungiyar da ke kiran kanta Kungiyar juyin juya hali ta Angola wato Angolan Revolutionary Movement ta hada da dalibai da kwararrun matasa ma'aikata, ta ce ta fusata saboda rushe gidaje da tada mutane da karfin tuwo da hukumomin kasar ke yi. Yayin da 'yan sanda kuma ke ci gaba da tursasa wa masu sana'o'i a bakin titi. Masu fafatukar za su kuma yi bore bisa bacewar biyu daga cikin takwarotinsu fiye da shekara daya da ta wuce. Sai kuma abin da ta kira gazawar gwamnati ta inganta rayuwar mafi yawa na 'yan kasar ta Angola mai arzikin man fetir. A makon da ya gabata 'yan sanda sun fada wa kafofin yada labarun cikin gida cewa zanga-zangar haramtacciya ce domin an shirya gudanar da ita a wani lokaci sabanin wanda doka ta tanadar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman