1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren neman sauyi a Saudiyya

Usman ShehuDecember 28, 2012

Jami'an tsaron Saudi Arabiya, sun bude wuta kan masu tarzumar adawa da gwamnati

https://p.dw.com/p/17AaB
Saudi Shiite protesters wearing masks chant slogans during a protest in Qatif, Saudi Arabia, Thursday, March 10, 2011. Saudi police have opened fire at a rally in the kingdom's east in an apparent escalation of efforts to stop planned protests.Government officials have warned they will take strong action if activists take to the streets after increasing calls for large protests around the oil-rich kingdom to press for democratic reforms. A witness in the eastern city of Qatif says gunfire and stun grenades were fired at several hundred protesters marching in the city streets Thursday. The witness, speaking on condition of anonymity because he feared government reprisal, said police in the area opened fire. The witness saw at least one protester injured. The small white signs at left in Arabic read: Freedom of expression is dignity to the nation.". (AP Photo)
Masu boren neman sauyi a kasar SaudiyyaHoto: AP

Yan sandan Saudi Arabiya sun bindige mutun guda har lahira a boren neman sauyi dake gudana a gabashin kasar. Mutumin da ya mutu a yau, shine cikamako mutane 12 wadanda jami'an tsaron Saudiya suka hallaka tun fara boren neman kifar da gwamnati, a dai-dai lokacin da ake zanga zanga a sauran kasashen Larabawa domin kawar da shugabannin kama karya. A kasar Saudiyya dai an fi gudanar da zanga-zanagar neman sauyi ne a gabashin kasar, inda yan Shi'a suka fi yawa, kana kuma jahar ta Qatif itace ta fi arzikin man fetur. Masu boren dai suna bore ne domin neman a sako dimbin yan fafitika wadanda jami'an tsaron Saudiyya suka kame, inda yan sanda suka bude wuta suka hallaka Ali Al-Marar ,dan sheakru 18 da haifuwa, kana suka raunata a kalla mutane shida. Kakakin yan sandan jahar yace yan sandan na kokarin kwantar da tarzumar da ake yi ne, inda mutane suka rufe hanya da tayoyin mota. A kasar Saudiyya dai ana yin boren neman sauyi tun sama da shekaru biyu, to amma ba da safai batun ke fitowa a kafa yada labaran duniya ba.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mouhamad Awal Balarabe