Boren 'yan adawa a kasar Zimbabuwe
March 23, 2017Gamayyar jam'iyyun adawa a kasar Zimbabwe sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Afirka ta AU da su kafa kwamitin da zai gudanar da zaben shugaban kasa da za a yi a kasar a badi. Shugabannin jam'iyyun adawar kasar Morgan Tsvangirai na jam'iyyar MDC da ma wasu, sun fadawa magoya bayansu da suka halarci gangamin adawa a birnin Harare jiya Laraba, cewar tilas ne a rusa hukumar zaben kasar. A cewar gamayyar masu adawar dai ba su yarda da martabar hukumar zaben kasar ba.
Shugaba Robert Mugabe na kasar mai shekaru 94 a duniya, na mulkin kasar yanzu shekaru 30, yana kuma shirin takara a zaben kasar na gaba. 'Yan adawar na kuma nuna turjiya ne ga sabbin matakan da gwamnatin Zimbawen ta dauka kan rijistar masu zabe, inda suka sha alwashin marawa Morgan Tsvangirai baya don fuskantar shugaba Mugabe.