1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren 'yan gudun hijira a Isra'ila

January 7, 2014

Dubban baƙin da ke neman inganta kare haƙƙinsu a Isra'ila, sun ƙuduri anniyar faɗaɗa zanga-zangar da suke yi don samun yanci

https://p.dw.com/p/1Amfu
Afrikanische Flüchtlinge demonstrieren in Israel
Hoto: Reuters

'Yan ƙasashen Afirka da ke zaman hijira a ƙasar Isra'ila, sun yanke shawarar tsawaita zanga-zangar da suke yi, don nemar wa kansu yanci. 'Yan gudun hijran, waɗanda akasari daga Afirka suka fito, sun bayyana cewa yanzu zanga-zangar da suka tsara yi na kwana uku, za su tsawaita ta, inda suke shirin yin mashi daga Tel Aviv izuwa birnin Ƙudus. Masu zanga-zangar dai, suna suka ne bisa yadda 'yan sandan ƙasar ta Isra'ila, ke ɗaure su a kurku ba bisa ƙa'ida ba, kana da yadda hukumomi suka ƙi basu matsayi na 'yan gudun hijira. Ita dai gwamnatin Isra'ila ta ce, baƙin ba wai 'yan gudun hijra bane, don haka baƙin haure ne kawai da suka shigo ƙasar ta ɓarauniyar hanya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Saleh Umar Saleh