Brazil da Afirka sun cimma matsayar tallafawa juna
July 4, 2010Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na ƙasar Brazil ya bayyana buƙatar samun haɗin kai a tsakanin ƙasar sa da Afirka domin cin gajiyar hakan a gaba. Shugaba Lula, wanda ya gudanar da wani taron ƙoli tare da shugabannin ƙungiyar kasuwar tarayyar yammacin Afirka ECOWAS a ƙasar Cape Verde ya ce makomar haɗin kan dake tsakanin Brazil da Afirka ta shafi zamnan lafiya da dai daiton lamura da kuma harkokin ci gaban ƙasa ne.
Lula ya kuma jaddada cewar, Brazil ce ƙasa ta biyu mafi yawan al'ummar baƙar fata a duniya baki ɗaya bayan Nijeriya, domin kuwa tana da baƙar fata da yawansu yakai miliyan 76 daga cikin al'ummar ƙasar da adadin su yakai miliyan 190.
A lokacin ganawar da ya yi da shugabannin ƙasashen na ECOWAS, waɗanda suka gudanar da taron yini ɗaya a tsibirin na Cape Verde, bayan kyakkyawan marhabin da suka yiwa shugaba Lula,shugaban Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan ya buƙaci samun haɗin kan Brazil wajen daƙile matsalar safarar muggan ƙwayoyi da makamai a yankin yammacin Afirka. S hi kuwa shugaban ƙasar Cape Verde Pedro Pires ya yi ƙira ne ga baiwa ƙasar Brazil kujerar din din a kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya.
Rangadin da shugaba Lula ke yi a nahiyar Afirka, za ta kaishi zuwa ƙasashen Equatorial Guinea, Kenya, Tanzania da kuma Zambia, kana ya halarci bukin rufe gasar cin kofin duniyar da Afirka ta kudu ke karɓar baƙunci duk kuwa da cewar, ƙasar sa ta fice daga gasar.
A lokacin wa'adi biyu na shugabancin Lula dai, dangantakar kasuwanci a tsakanin Brazil da Afirka ta ninka - har sau ukku - idan aka kwatanta da gabanin mulkin nasa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh