1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil: Shugaba Bolsonaro ya kama aiki

Gazali Abdou Tasawa MNA
January 2, 2019

A jawabinsa na kama aiki a ranar Talata, sabon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya sha alwashin yaki da masu muggan ayyuka da cin hanci da kuma kawar da akidar gurguzu daga kasar.

https://p.dw.com/p/3AsbU
Brasilien | Amtseinführung Jair Bolsonaro
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/S. Izquierdo

Sabon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya sha alwashin maido da doka da oda a kasar, ta hanyar shiga kafar wando daya da masu muggan ayyuka da kuma musamman yakar cin hanci da rashawa da kuma kawar da akidar gurguzu. Shugaban mai akidar kyamar baki, tsohon soji mai shekaru 63, ya bayyana wannan aniya tasa ce a gaban dubban 'yan kasar a jawabinsa na ranar farko ta kama aikin shugabancin kasar na tsawon wa'adin shekaru hudu.

Bolsonaro ya yi alkawarin kawar da akidar da ke bayar da kariya ga tsageru tana kuma hukunta 'yan sanda. Matsalar da shugaban ya ce ta yi sanadiyyar mutuwar 'yan Brazil da dama da ba su ji ba su gani ba.

Shugaba Bolsonaro ya kuma bayar da shawarar cimma yarjejeniyar samun fahimtar juna tsakanin al'umma da bangaren zartarwa da na majalisa da kuma na shari'ar domin ci-gaban kasar.

Da kimanin kaso 55 daga cikin 100 Shugaba Bolsonaro ya lashe zaben da kasar ta shirya a ranar 28 ga watan Oktoban da ya gabata.