Dakile aikin masu tarzoma a Brazil
January 6, 2019Talla
Kusan 'yan sanda 300 ne aka jibge a birnin Fortaleza da ke zama babban birnin jihar ta Ceara da wasu birane sama da goma, ganin yadda a tsawon kwanaki hudu ake ganin kone-kone da lalata kadarorin gwamnati kamar yadda sakataren yada labaran gwamnatin kasar ta Brazil Guilherme Teophilo ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Agencia Brasil.
Yayin da ake bincike kan musabbabi na ta da hargitsin wasu rahotanni dai sun nunar da cewa cikin dalilai na ta da hargitsin har da batun kara tsaurara matakai na tsaro a gidajen kaso na kasar. Wannan dai na zama gwaji na kamun ludayi ga sabon shugaban kasar Jair Bolsonaro da aka rantsar a ranar Talatar da ta gabata.