SiyasaJamus
Amurka za ta bude iyakokinta Mexko da Kanada
October 13, 2021Talla
Amurka za ta sake bude iyakokinta na kasa ga kasashen Mexiko da Kanada ga wadanda aka yi wa alluran rigakafin corona daga farkon watan gobe. Wani kusa a fadar White House ne ya bayyana haka a wannan Laraba, a ci gaba da sakin mara wa tsauraran matakan kariya da annobar corona da ta yi mumunan illa ga kasar.
Tun a cikin watan Satumban da ya gabata, gwamnatin Amurka ta ambaci shirin bude iyakokinta na sama ga wasu kasashen nahiyar Turai da Birtaniya ga suka yi alluran rigakafin cutar shekara daya da rabi bayan da kasar ta takaita shigar 'yan kasashen karkashin gwamnatin tsohon shugaba Donald Trump.