Hatice ta kadu da ganawar Macron da Yerima
July 28, 2022Talla
Yayin da Yeriman Saudiyya mai jiran gado Mohammad bin Salma, ya fara ziyara a Faransa a karon farko tun bayan kisan fitaccen dan jarida Jamal Khashoggi, budurwar marigayin Hatice Cengiz wacce yar asalin kasar Turkiyya ce inda aka kashe Khashoggi, ta yi tir da matakin Shugaban Farnsa Emmanuel Macron na marabtar Yerima bin Salman.
Hatice Cengiz ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, abin kunya ne da takaici na jin labarin Shugaba Macron zai karrama wanda ya kashe mijinta wato Jamal Khashoggi.
Yerima bin Salman dai ya nesanta kansa da hannu a zargin kashe dan jaridar Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santanbul a kasar Turkiyya a shekarar 2018.