Buhari ya caccaki Myanmar a taron duniya
September 19, 2017Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a wannan rana ta Talata ya kwatanta tashin hankali da ke faruwa a kasar Myanmar inda soja ke gallazawa al'ummar Musulmi marasa rinjaye na Rohingya da cewa tamkar kisan kiyashi ne da ya faru a Bosniya da Ruwanda, inda ya bukaci da a tsayar da duk wani kokari na kawar da wata al'umma a doran kasa don bada dama ga 'yan gudun hijira su koma kasarsu ta haihuwa.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga taron shugabanni na duniya da ke halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, ya ce abin da ke faruwa a Myanmar ba maraba da abin da ya faru a Bosniya a shekarar 1995 da abin da ya faru a shekarar 1994 a Ruwanda.
Ya ce lamarin kasar ta Myanmar abin tada hankula ne da ya faru wanda kuma gwamnatin kasar na da masaniya a kokarinta na ganin an rage yawan al'ummar Rohingya saboda dalili na addini da kabila.