Siriya: Bukatar gudanar da sahihin zabe
December 18, 2024Cikin wannan wata na Disamba da muke ne 'yan tawaye suka kifar da gwamnatin ta Bashar al-Assad, abin da ya sanya jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniyar a Siriya Geir Pedersen ya bukaci da a gudanar da sahihin zabe tare da yin kiran kai daukin gaggawa na agajin jin-kai ga kasar da yaki ya daidaidata. Da yake jawabi ga manema labarai a Damascus babban birnin kasar ta Siriya Pedersen ya ce, a yanzu akwai alamun samar da sabuwar Siriya da yake fatan za ta kawo mafita ta siyasa har ma a yankin Arewa maso Gabashi da Kurdawa ke jagoranta. Ya kuma yi kira da a samar da sabuwar Siriya da za ta yi amfani da kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na 2254 da aka samar a 2015, wadda za ta fitar da sabon kundin tsarin mulki da gudanar da sahihin zabe bayan wa'adin gwamnatin rikon kwarya ya kawo karshe.