1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nato ta bukaci girmama yarjejeniyar hatsi

Abdoulaye Mamane Amadou
August 1, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai da NATO, sun yi kira da a mutunta yarjejeniyar fitar da hatsi da kasashen Ukraine da Rasha da suka rattaba wa hannu a birnin Istanbul karkashin jagorancin Turkiyya.

https://p.dw.com/p/4EyLU
Russland - Ukraine Krieg
Hoto: Michael Shtekel/AP/picture alliance

Da yake tsokaci game da batun babban jami'in diflomasiyar harkokin wajen tarayyar Turai Josep Borrell, ya jaddada cewa nahiyar Turai na dakon ganin bangarorin biyu sun mutunta yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine don wadata duniya da ta fada cikin wani garari sakamakon toshe hanyoyin fitar da hatsin da kasar Rasha ta yi.

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya jinjina wa Turkiyya kan matakin da ta dauka na shiga tsakani har aka cimma wannan matsaya.

A wannan Larabar ce ake dakon isar jirgin ruwa dauke da hatsi ton dubu 26 da ya tashi daga gabar ruwa ta Odessa ta kasar Ukraine zuwa Lebanon, matakin farko na soma yarjejeniyar fitar da hatsi da aka kulla tsakanin Ukraine da Rasha a ranar 22 ga watan Yuli na 2022.