Bukatar tallafin Jamus a kan tsaro
October 31, 2023Talla
Akufo-Addo ya ce ayyukan ta'addanci na zama babbar barazana a Yammacin Afirka, inda 'yan jihadi suka bazu a yankin Sahel baki daya. Shugaban kasar ta Ghana ya kara da cewa, a baya kasar Mali ce kawai ake da 'yan ta'adda mafi karfi, amma yanzu sannu a hankali ayyukan ta'addanci na neman zama babbar barazana a Yammacin Afirka baki daya. Ya kuma kwantanta kasar Jamus a matsayin babbar kawa a fannin tsaro, don haka Akufo-Addo yace yana fatan Jamus za ta bada tallafin kayan soja musamman a bangaren leken asiri. Kasar Ghana dai ita ce ta karshe a ziyarar kwanaki uku da shugaban gwamnatin Jamus ya kai Yammacin Afirka, inda ya fara da Tarayyar Najeriya.