Bukatar Turkiya
March 16, 2012A sakamakon karuwar yawan 'yan gudun hijrar Siriya da ke kwarara zuwa Turkiya, fraiministan kasar, Reccep Tayyip Erdogan ya bayyanar da bukatar kebe wani yanki kusa da iyakar kasashen biyu domin kare 'yan gudun hijrar. Erdogan ya kara cewa zai janye jakadansa daga Siriya da zaran mutanen kasarsa sun bar kasar. Ma'aikatar harkokin wajen Turkiya ta yi kira ga dukan 'ya'yanta da ke Siriya da su fice daga wannan kasa. A dai halin yanzu kasashe mambobin kungiyar hadin-gwiwar yankin Gulf sun rufe ma'aikatun jadancinsu da ke birnin Damaskus. A cikin wata sanarawar hadin-gwiwa da suka bayar sarakunan kasashen yankin Gulf guda shida sun soki Shugaba Bashar al Assad da kashe al'umar kasarsa da kuma yin fatali da duk wani shiri na samun mafita daga rikicin siyasar kasar. Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane dubu 8 suka rasa rayukansu a kasar ta Siriya tun bayan ta boren nuna adawa da gwamnati shekara guda da ta gabata.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi