1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar zagaye na biyu a zaben Senegal

March 2, 2012

Senegal da Afirka ta kudu da Somalia sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/14DBW
Senegalese President Abdoulaye Wade addresses journalists during a press conference at the presidential palace in Dakar, Senegal Monday, Feb. 27, 2012. As votes were being tallied on Monday from Senegal's Sunday presidential election, leading opposition candidate Macky Sall declared that no candidate had gotten the necessary 50 percent, making a runoff "inevitable." (Foto:Rebecca Blackwell/AP/dapd)
Shugaban Senegal Abdoulaye WadeHoto: AP

To madallah. Mafi yawan jaridun na Jamus a wannan mako sun maida hankalin su ne kan al'amura masu daukar hankali  a nahiyar Afrika da suka hada har da  zaben  shugaban kasa a Senegal, inda   aka ga alamun cewar sai an kai ga zagaye na biyu  tsakanin shugaba Abdoulaye Wade da abokin taiarar sa, ko kuma  matakin da jam'iyar ANC dake mulki a Afirka ta kudu ta dauka na koran shugaban  reshen matasa na jam'iyar Julius Malema, wanda aka dade ana takaddama kansa saboda aiyukan sa na bata  mata suna, sai kuma kasar Somalia, inda batun zaman lafiya ya gagara, duk kuwa da taron da kasashe suka gudanar a London na neman  binciko hanyoyin warware halin yaki da kasar take ciki.

Jaridar Süddeutsche Zeitung  tayi sharhi a game da zaben shugaban kasa a Senegal, inda tace wannan zabe ya sabawa al'ada a nahiyar Afirka, inda  a duk lokacin da aka zo zabe sai an zub da jini. A  Senegal ko da shike  an ga alamun tilas a kai ga zagaye na biyu na zaben, amma  akalla  ba'a sami kashe-kashe ba. Duk da adawa mai yawa, amma Abdoulaye Wade, dan shekaru 85 da haihuwa ya tsaya kai da fata sai ya sake wa'adi na uku, duk da cewar kundin tsarin mulkin kasar ta Senegal bai yarda da haka ba. Mai adawa dashi, Macky Sall, shekarun sa 50 ne kawai da haihuwa, kuma da alama shi al'ummar kasar, musamman yan adawa da matasa suka  fi son ganin ya kama mulki. Duk da haka, inji jaridar  Süddeutsche Zeitung, Wade ya tara manema labarai inda yace shine kan gaba bayan kidaya kuri'u da kashi 35 cikin dari, Sall kuma yake da kashi 26 cikin dari na kuri'un da aka kada.

 Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta sharhinta ne a game da takaddamar dake tsakanin jam'iyar dake mulki a Afirka ta kudu, wato ANC  da shugaban reshen matasa na jam'iyar, Julius Malema, wanda bayan  sabani na lokaci mai tsawo, aka kore shi daga   wannan jam'iya saboda matakan sa na bata sunan jam'iyar. Jaridar ta ambaci  wata sanarwa daga kwamitin ladabtarwa na ANC dake cewar wannan mataki an dauke shi ne  saboda Malema yaki yarda da   zargin cewar  ya aikata ba daidai ba,  a duka matakan da yake dauka na bata sunan  jam'iyar tun daga watannin baya. Daga cikin laifukan da aka zargi Malema  tattare dasu, har da fita fili yayi kiran kayar da gwamnatin makwanciyar kasar Botswana, ya kuma kara zafafa  sukan sa kan shugaban kasa Jacob Zuma. To sai dai jaridar  Frankfurter Allgemeine Zeitung tace koran Malema daga ANC ba zai zama karshen zamanin sa na siyasa ba, saboda yana da matukar farin jini tsakanin matasa, wadanda suke ganin sa a matsayin  abin misali a jam'iyar ta ANC.

ARCHIV - Der Chef der Jugendliga des Afrikanischen Nationalkongress (ANC), Julius Malema, aufgenommen am 20.09.2010 in Durban. Die südafrikanische Regierungspartei ANC hat die Suspendierung des Parteirebellen Julius Malema vorläufig bestätigt: Der Chef der ANC-Jugendliga habe dem Ansehen der Partei tatsächlich geschadet, so der Disziplinarausschuss des ANC am Samstag (04.02.2012) in Pretoria. Foto: Jon Hrusa dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++
Julius Malema shugaban reshen matasa na ANC a Afirka Ta KuduHoto: picture-alliance/dpa

A makon jiya, aka gudanar da  taron kasashe sittin da masu  ruwa da tsaki a kokarin ganin an sami zaman lafiya a Somalia. Wannan taro da kuma halin da kasar ta yankin kahon Afirka take ciki, ya baiwa jaridar Die Tageszeitung damar  sharhi game da  halin da yan gudun hijira suke ciki a sansani mafi girma   a duniya dake Dadaab a arewacin Kenya. Jaridar tace  kungiyar likitocin duniya ta baiyana matukar damuwa a game da halin da sansanin yake ciki, musamman game da kara munin yanayin zama a cikin sa Ita ma hukumar yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tayi gargadin cewar  yan gudun hijira  dubu  463 dake  zaune a sansanin na Dadaab  nan gaba kadan kasancewra su a can zai gagara, sai fa idan an dauki matakan gagawa na gyara. Yayin da aka maida hankali  ga ita kanta Somalia,  ba kuma za'a iya kau da idanu game da matsayin  dimbin yan gudun hijira da suka tsare daga kasar suke zaune a sansanoni a ketare ba.

dozens of cares from Elasha Biyaha loaded with properties of fleeing people Fotokorrespondent: Abdulkadir Foodey
Yan gudun hijiran SomaliaHoto: DW

Da wannan sharhi na jaridar  Die Tageszeitung  muka zo karshen shirin na Afrika a jaridun Jamus na wannan mako.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Muhammad Nasiru Awal