Bukin ranar muhalli ta duniya
June 5, 2006Talla
MDD ta yi gargadi cewa yankunan hamada ka iya fadada cikin lokaci kankani a duniya baki daya. A cikin jawabin sa ga ranar muhalli ta duniya wadda ake yi yau litinin, babban sakataren MDD Kofi Annan ya ce yanzu haka hamada ta rufe kashi daya cikin uku na doron kasa baki daya, kuma a halin da ake ciki wasu yankunan na fuskantar barazanar bushewa saboda kwararowar hamada. Annan ya ce yankin kudu da Sahara da yankin kudu maso gabashin nahiyar Asiya sun fi fuskantar barazanar kwararowar hamadar. Sakataren na MDD ya kara da cewa matsalar gusowar hamadar na zama babban cikas ga yakin da ake yi da talauci.