Nijar: A karon farko Tiani ya halarci Sallah Idi
April 9, 2024Talla
Babban limamin kasar Nijar Sheick Karantaya jagoranci sallar karamin idin ta shekarar bana, kuma a hudubar da ya gabatar ya jan hankalin al’umma da magabata kan muhimmancin hadin kai da son kasa ta la’akari da yanayin da kasar.
Abdpurahamane Tiani ya halarci Sallah Idi
Shugaban hukumar mulkin soja shugaban kasa Janar Abdourahmane Tiani wanda jama’a suka yi ta dora ayar tambaya kan ko zai halarci sallar idin da ke zama ta farko a gare shi tun bayan da ya karbe mulki, bai yi kasa a gwiwa ba wajen ya halarci sallar idin tare da sauran mambobin majalisar mulkin soja ta CNSP da kuma mambobin gwamnatinsa .