Burkina Faso: An yanke hukuncin kaso ga wasu attajirai
July 21, 2017A kasar Burkina Faso wata kotun birnin Ouagadougou ta yanke hukuncin dauri na shekaru uku-uku ga wasu manyan attajiran kasar bayan da ta same su da laifin yin wata hada-hadar kudi ta boge da ta ba su damar samun miliyoyin kudaden cefa.
Daga cikin manyan 'yan kasuwar kasar ta Burkina Faso da hukuncin ya hau kansu har da Sayouba Zidwemba da ake yi wa lakabin "Will Telecom" da ya yi suna a fannin kasuwancin na'urori da kayan latroni, da kuma wasu attajiran su 10 wadanda kotun ta samu su da laifin yin takardun boge da suka basu damar zare daga cikin asusun ajiyarsu kudadensu miliyan 20 zuwa 67 na cefa da suka danfari bankin kasashen Afirka ta Yamma na CBAO da ke da ciyarsa a Senegal.
A watan Febrarun da ya gabata ne dai wani bincike da bankin na CBAO ya yi ya bankado badakalar kudi ta kusan miliyan dubu 200 na cefa da aka yi danfararsu daga bankin zuwa wasu kasashen Afirka ta Yamma da suka hada da Cote d'Ivoire da Burkina Faso.