Burtaniya na fuskantar kalubalen tsaro
November 24, 2014Sakatariyar harkokin cikin gidan Burtaniyar Theresa May ta ce jami'an tsaron kasar sun tabbatar musu cewar lamuran tsaron kasar na fuskantar wannan kalubale ne daga 'yan ta'adda don haka abu ne da May din ta ce ya kyautu a dauka da muhimmancin gaske.
Ms. May ta ce a saboda haka ne ma London za ta dauki matakai na ganin ta dakile duk wani aiki na ta'addanci kuma ma tuni ta kammala shirye-shirye na mika wani kuduri ga majalisar dokokin kasar wanda ya danganci yaki da ta'addanci.
Kudurin dai inji sakatariyar harkokin cikin gidan ya hada da dabaru na kawar da duk wata barazana da za a iya fuskanta daga 'yan kasar da suka dawo gida daga Siriya da Iraki musamman ma wanda suka tallafawa kungiyar nan ta IS a fafutukarta ta kafa daular Musulunci.