1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burtaniya za ta shiga yakin da ake da IS

Ahmed SalisuSeptember 26, 2014

Majalisar dokokin Burtaniya ta kada kuri'ar amincewa da shiga yakin da Amirka ke jagoranta kan 'yan kungiyar nan ta IS da ke rajin kafa daular Musulunci a kasar Siriya da Iraki.

https://p.dw.com/p/1DLpq
britischer Soldaten während des Irak Krieges 2004
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb

A wani zama da ta yi dazu, majalisar ta amince da gagarimin rinjaye kan sojin Burtaniya su shiga a dama da su wajen ganin bayan 'yan kungiyar don ganin ba su kai ga fadada wuraren da suke kamawa ba.

Gabannin amincewar da 'yan majalisar suka yi na shiga yakin, firaministan kasar David Cameron ya ce in aka bar kungiyar ta cigaba da aiyyukan ta to kuwa za a fuskanci baraza babba daga daular 'yan ta'adda a gabar tekun Mediterranean.

Yanzu haka dai sojin saman Burtaniya za su shiga sahun takwarorinsu na Amirka da Faransa da Saudi Arabiya da Hadaddadiyar Daular Larabawa da Bahrain da kuma Jordan a kokarinsu na kawar kungiyar.