Burundi : An kashe ministan muhalli
January 1, 2017Talla
'Yan sanda sun ce an kashe ministan dan shekaru 54 a lokacin da ya ke dawo gida a daran jiya, sai dai sun ce sun kame wata mata da ke tare da shi cikin mota a lokacin da harin ya afku. Wannan hari shi ne na farko da aka kai a kan wani ministan a Burundi tun lokacin da kasar ta fada cikin wani hali na rikicin siyasa bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya yi tazarce.