1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cafke masu hannu a harin Peshawar

December 21, 2014

Ministan harkokin cikin gida na kasar Pakistan Chaudhry Nisar Ali Khan ya ce sun cafke wasu mutane da suke zargi da hannu a mummunan harin da aka kai a garin Peshawar.

https://p.dw.com/p/1E8MH
Hoto: Reuters/Pakistan Taliban

'Yan kungiyar ta'addan Taliban ne dai suka kai harin a wata makaranta da ke garin Peshawar na kasar tare da hallaka mutane 148 mafi yawa kananan yara dalibai. Ali Khan ya bayyana cewa hukumomin kasar sun cafke mutane da dama koda yake bai bayyana ko wadanne irin mutane suka kama ba.

Kungiyar ta Taliban dai ta da dauki alhakin kai wannan hari, ta bayyana cewa ta kai shi ne domin daukar fansa dangane da farmakin da dakarun gwamnati suka kaddamar a kan kungiyar a yankin arewacin gundumar Waziristan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo