Ana cece-kuce a Saudiya kan mahajar karin aure
November 23, 2021
Cece kucen da ake yi Saudiya dangane da wata bita da wata ƙungiya ta shirya gabatarwa kan koyar wa maza dabarun ƙarin aure ya jawo sukar wannan bitar da ke ci gaba da jawo mahawara.
Wata ƙungiya ce ta Al-Bir ta shirya horas da maza a hedikwatarta da ke Ar-Rass na Saudiyya a darasin da aka yi wa taken "dubarun ƙara mace ta biyu" da zimmar karawa mazan da ke taraddudn karin aure karfin gwiwar ida aniyarsu, don cin moriyar da ke cikin karin auren.
Matakin ya gamu da fushin ƴan Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa inda suka dinga tsokaci a kafofin sadarwa na intanet. An dai samu ra'ayoyi masu cin karo da juna kan darasin amma yawancin na suka sun fi yawa, inda wasu ke ganin darussa na yadda za su samu ayyukan yi ne ko digiri na biyu da na uku ya kamata a koya masu amma sun yi mamakin ɓullo da wannan darasin a wannan lokacin. Mafi yawanci tsokacin mutane na nuna ɓacin rai ne game da sanarwar.
Wasu ƴan Saudiyya na ganin ƙarin aure halal ne kuma yana da sharuɗɗa, abin da yake da muhimmanci shi ne idan mutum zai iya tabbatar da adalci kuma yana da arzikin kula da mata biyu. Don haka babu wani darasi da ake buƙata.