1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece-kuce kan gidajen alkalai

November 15, 2024

A farkon wannan mako ne matakin ministan babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja Nyesom Wike na kwace wani fili mallakin kamfanin Julius Berger, tare da gina unguwar alkalai ya jawo yamutse hazo cikin kasar.

https://p.dw.com/p/4mzw8
Najeriya I Ezenwo Nyesom Wike | Minista | Alkalai | Gidaje
Ministan Abuja fadar gwamnatin Tarayyar NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Naira miliyan 6000 ne dai ministan ya ce ya kashe wajen gina unguwar da ta kunshi gidajen alkalai, wadanda Nyesom Wike ya ce suna zaman kyauta daga gwamnatin tarayyar. Kyautar kuma da yanzu haka ke jawo kace-nace cikin kasar, inda mafi yawan 'ya'yanta ke fadin ana shirin saye alkalan. Duk da cewar dai babbar alkali ta kasar ta ce gidajen na iya taimakon alkalan samun nutsuwar sauke nauyi, manya da ma kananan lauyoyi ko bayan masu takama da yakin hancin kasar na kallon kyautar da idanun kokarin rushe 'yancin shari'a a Najeriyar. Barrister Mohammed Saidu Tudun Wada dai na zaman shugaban kungiyar Lauyoyi Musulmi a kasar, kuma ya ce dokokin da ke cikin kasar sun tabbatar da haramcin duk wata kyauta zuwa gidan alkalan. Kama daga rikicin rusau da ke a birnin yanzu ya zuwa na siyasar PDP ko bayan rawar da ya taka a cikin mulkin jiharsa ta Rivers dai, Wike na zaman na kan gaba a cikin rigingimun da ke gaban alkalan Najeriyar a halin yanzu.

Babandede ya yi tir da cin hanci a Najeriya

Akwai dai tsoron matakin ka iya janyo son zuciya cikin jerin shari'un, koma rushe ingancin shari'un da ke kotunan kasar dabam-dabam. Kokarin kaucewa hanci cikin gidan alakalan ne dai ya kai ga ninka yawan albashin yan shari'ar, daga bangaren gwamnatin tarayyar a farko na shekarar bana. Auwal Musa Rafsanjani dai na zaman shugaba na kungiyar Transparency in Nigeria mai yakiar cin-hancin, kuma ya ce akwai hadari na jirkita tunanin alkalan cikin batun kyautar ta Wike. Koma wane tasiri goron na ministan yake shirin yi a gidan alkalan dai, ministan ya ce yana kokarin sauke nauyin shugaban kasar da ya dauki lokaci yana danyen ganye da manyan alkalan kasar. Kuma matakin gwamnatin kasar dai, na da shirin taimakawa alkalai na kasar da ke cikin matsin kudi. Da ma dai an dade ana zargin alkalan da komawa 'yan amshin shata na bangaren zartarwar, a cikin wani tsarin da ke kallon karkatar da jerin shari'u zuwa wani yanayin kana gani kana dada rudewa.