1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Trump ya cire wani sakon da ya wallafa

Binta Aliyu Zurmi
June 28, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ya cire wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter wanda ke dauke da bayanan da ke nuna fifikon da farar fatar kasar ke da shi a kasar Amirka.

https://p.dw.com/p/3eTRd
USA Wahlkampfveranstaltung Trump in Tulsa
Hoto: Getty Images/AFP/W. McNamee

Cire wannan sako da shugaban ya yi ya biyo bayan zarginsa da aka yi da ruruta wutar nuna kyama ga bakaken fata. A cikin sakon wanda na bidiyo ne, an jiyo magoya bayansa na rera wasu kalamai wanda masu tsananin kyamar baki ke amfani da shi.

A lokuta da dama dai irin wannan kalamai sun janyo suka daga cikin magoya bayan jamiyyar Republican ta Shugaba Trump din.

Wannan dai na zuwa ne makwanni kalilan bayan da kasar ta hargitse sakamakon kisan da wani dan sanda ya yi wa wani dan kasar bakar fata wato George Floyd, wanda hakan ya haifar da zanga-zanga mai tsanani a ciki da wajen kasar