131108 Grüne Özdemir Parteivorsitz
November 18, 2008Cem Özdemir shi ne Baturke na farko da ya taɓa samun wannan muƙami a nan Jamus. Hakazalika shi ne na farko da wata babbar jam´iyar adawa ta taɓa naɗawa a wannan muƙami. Da yawan ƙuri´u 79.2 cikin 100 ´ya´yan jam´yiar sun goya masa baya. Ko shin wane ne Cem Özdemir? Shirin Mu Kewaya Turai na wannan makon zai duba tarihi da kuma matsayin wannan ɗan siyasa a nan Jamus.
Sabon shugaban na jam´iyar The Greens ke nan Cem Özdemir bayan ya da aka zaɓe shi akan wannan muƙami, inda ya ke cewa:
“Zan haɗa ƙarfi da ku domin mu yi yaƙin samar da wata al´umma wadda za ta girmama kowa da kowa ba tare da la´akari da asalinsa ko ƙasar da iyayensa ko kakanensa suka fito ba. Mu kam ba ma nuna banbanci, a garemu kowa abu guda ne kuma dukkanmu muna da muhimmanci.”
Cem Özdemir mai shekaru 42, a cikin shekarun 1960 iyayensa suka yo ƙaura daga Turkiya zuwa yankin kudancin Jamus, inda a nan ne kuma ya girma. Ya shafe shekaru 25 a cikin jam´iyar The Greens kuma ya san kowane lungu da saƙo na wannan jam´iya. Shi ne wakilin jam´iyar a majalisar dokokin Turai. Gabanin babban taron jam´iyar Özdemir ya sha kaye a ƙoƙarinsa na neman jam´iyar ta tsayar da shi a matsayin ɗan takarar neman kujerar majalisar dokoki ta Bundestag a zaɓen da za a yi a baɗi. Tsohon shugaban jam´iyar Reinhard Bütikofer ya bayyana wannan kaye na farko da Özdemir ya sha da cewa ko kaɗan bai karya masa ƙarfin guiwar cimma muradinsa.
“Gaskiya wannan kaye da ya sha bai sa yayi ƙasa a guiwa ba. Rashin yin haka ya tabbatar mana da cewa shi mutum ne mai ƙwazo wanda zai yiwa wannan jam´iya jagoranci na gari.”
Ko da yake Cem Özdemir ya ɗan yi shakka amma bai janye takararsa ta neman shugabancin jam´iyar ba. Wani abin da ya sa jam´iyar ta yi fice shi ne rarrabewa da take tsakanin masu riƙe da muƙami a cikinta da wakilanta a majalisun dokoki, domin kaucewa samun wani shugaba mai cikakken iko. Amma duk da haka Özdemir na mai ra´ayin cewa jam´iyar ka iya bawa shugabanninta wata daraja da ta dace.
“Ina ganin ya zama wajibi ka yi aiki da abin da kake faɗi. Wannan ya haɗa da yadda ake tafiyar da abubuwa ciki har da shugabancin wannan jam´iya. Ya kamata mu yi amfani da dokokinmu. Bai kamata mu riƙa ganin juna a matsayin abokan hamaiyar ko waɗanda ke faɗa da juna ba.”
Ƙiris ya rage da jam´yiar ta The Greens wadda kanta ke adawa da tsarin shugabanci na kai ne wuƙa kai ne nama, ta faɗa cikin wannan tsari wajen zaɓan wanda zai gaji tsohon shugabanta Reinhard Bütikofer, domin da farko dukkan ´yan takara sun so janyewa, abin da ke nuni da rashin karsashi na wannan muƙami. Ba wani abin da ya kawo ciƙas ga zaɓen Özdemir wanda ke zama Baturke kuma musulmi na farko da ya ɗare kan kujerar shugaban wata babbar jam´iya a nan Jamus.
Tun a shekarar 1994 Özdemir masani a fannin reno da zaman jama´a, aka ya shiga majalisar dokoki ta Bundestag a matsayin Bajamushen farko mai asali da ƙasar Turkiya. A majalisar Özdemir ya mayar da hankali a fannin zaman baƙi da zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka. Hakan ya ƙara masa farin jini a tsakanin ilahirin ´yan siyasan wannan ƙasa. A shekara ta 2002 ya yi murabus saboda yayi amfani da tikitin jirgin sama na aiki don biyan buƙatun kansa. Yanzu haka dai shi ne wakilin jam´yiar The Greens a majalisar dokoki Turai.
Babban ƙalubale na farko ga sabon shugaban dai shi ne yaƙin neman zaɓen ´yan majalisar dokoki da za a yi shekara ta 2009. Wannan ba ƙaramin aiki ba ne ga wannan jam´iyar adawa wadda ke son ta yi amfani da batutuwan da sabon shugaban nata ya bayyana su da cewa sun ɗan kaucewa manufar su a da, wato kamar adawa da makamashin nukiliya da kare muhalli.
“Yanzu haka dai a nan Jamus ana yabon shugabar gwamnati a matsayin wata shugabar kare muhalli. Amma idan muka kalli abin daga birnin Brussels za mu ga cewa yayi muni ƙwarai da gaske. Mutuncin shugabar gwamnatin na zubewa a idanun mu.”
Cem Özdemir wanda a tsakanin jam´iyar yake cikin ɓangaren waɗanda ake kira Realos wato waɗanda suka fi ba da la´akari da manufofin siyasa na zahiri maimakon wasu manufofin da jam´iya ta tsara tun da farkon fari, dole zai bi sahun magabacinsa Reinhard Bütikofer, wato wani shugaban jam´iyar da ba ya da kujera a majalisar dokoki. Ko shakka babu hakan zai taƙaita angizonsa.
Abokiyar shugabancisa a wannan muƙami ita ce Claudia Roth mai ra´ayin canji wadda kuma ke da farin jini a tsakanin ´ya´yan jam´iyar. Ta yi nuni da cewa ta aiki tare ne za a samu nasara a wannan jam´iya wadda a halin yanzu take ƙara samun yawan magoya baya.
A ɓangaren Turkawa da suka ga na su ya samu shiga cikin harkokin siyasa gadan gadan a nan Jamus sun bayyana shi a matsayin wani Obama na su, suna cewa wannan nasara ta sa ta yi daidai da nasarar da wadda Obama ya samu a Amirka saboda haka shi Özdemir Obama ne a garesu.
Ko shakka babu jam´iyar ta The Greens ta kafa tarihi fagen siyasar wannan ƙasa sakamakon zaɓen Cem Özdemir a matsayin shugabanta. Saura da me yanzu dai an zura ido a ga kamun ludaiyinsa ko wataƙila wasu jam´iyun za su yi koyi da wannan mataki na The Greens.