1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta hana ayyukan hakar Zinare a Arewa

Salissou Boukari
August 16, 2018

Gwamnatin kasar Chadi ta baiwa rundunar Sojojin kasar umarnin korar dukannin masu ayyukan hakar zinare a yankin Miski da kuma Kouri Bourgri da ke jihar Tibesti a yankin Arewa mai nisa na kasar.

https://p.dw.com/p/33Gzd
Sahel Konflikt - Malische Armee
Hoto: Getty Images/AFP/D. Benoit

Ministan tsaron kasar ta Chadi Ahmat Bachir ne ya sanar da matakin ta kafofin yada labarai na kasar ta Chadi inda ya ce sun ba wa sojojin kasar na sama da ma na kasa umarnin su fitar da dukannin masu hakar zinaren tare da ragargaza manyan injinan da ke wurin, da tankokin mai ko na ruwa tare da kone dukannin shagunan da ke wurin da ma kayayakin masu hakar zinaren. Sojojin kuma sun samu izinin kame duk wanda suka samu ya na shawagi a yankin.

A ranar Asabar ce dai wani ayyarin motoci kimanin 100 dauke da manyan bindigogi da suka fito daga kasar Libiya, suka kai hari a Kouri Bourgri, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar ta Chadi uku cikinsu har da wani kanal na soja.