SiyasaAfirka
Rundunar sojin Chadi na neman ma'aikata
September 25, 2021Talla
A yayin da yake magana a gaban Majalisar Dokoki a ranar Jumma'a, Ministan Tsaron Kasar Daoud Yaya Brahim ya ce rundunar sojin Chadi tuni ta fara yunkurin daukar matasan kasar aiki, inda ta fara da daukar sabbin kananan sojoji.
Brahim ya ce manufar hakan ita ce karfafa rundunar sojin Chadi yadda za ta iya tunkarar kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta da bayar da gudunmmawa a yakin da ake yi da 'yan ta'adda a kasashen Sahel.
A cikin gida, kasar ta Chadi na fuskantar gagarumar matsalar tsaro daga 'yan tawaye a arewacin kasar. A watan Afrilun da ya gabata Tsohon Shugaban Kasar Idriss Deby ya rasa ransa a fagen daga a yayin da ya kai ziyara ga dakarun kasar da ke yaki da 'yan tawayen da suka shigo Chadi daga kasar Libya.