1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta yi watsi zargin dagula zaben Amirka

Suleiman Babayo AS
September 26, 2018

Gwamnatin kasar Chaina ta yi watsi da batun Shugaba Donald Trump na Amirka bisa cewa tana neman kutse a zaben Amirka da ke tafe.

https://p.dw.com/p/35Y3i
Präsident Donald Trump nimmt an einem Sicherheitsrat der Vereinten Nationen teil
Hoto: picture-alliance/E.Vucci

Kasar Chaina ta yi watsi da zargin da Shugaba Shugaba Donald Trump ya yi mata cewa tana shisshigi a harkokin zaben Amirka da ke tafe a watan Nuwamba na majalisar dokoki. Ministan harkokin wajen kasar ta Chaina Wang Yi ya musanta kalaman na Shugaba Trump.

Tun farko Shugaba Donald Trump na Amirka lokacin da ya jagoranci zaman Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duiniya ya zargi kasar Chaina da neman zagon kasa musamman domin nakasa bangaren Trump lokacin zaben, inda Shugaba Trump ya kara da cewa:

"Lokacin jawabin da na gabatar jiya (Litinin) a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, na nuna hanyar da gwamnatinmu ke bi domin tabbatar da ganin zaman lafiya. Abun takaici shi ne Chaina tana kokarin yi mana shisshigi lokacin zaben watan Numawan na wannan shekara ta 2018. Ba sa son bangare na ya samu nasara, saboda ni ne shugaban kasa na farko da ya kalubalanci Chaina kan kasuwanci, kuma muna samun nasara a kowane mataki. Ba ma son su shiga mana harkokin zaben da ke tafe."

Kana shugaban na Amirka ya nuna gamsuwa da irin ci-gaba da aka samu da Koriya ta Arewa kan hanyoyin neman raba kasar da makaman nukiliya.