Charles Taylor da kotun kasa da kasa dake Hague
April 1, 2006Talla
Mdd na nan na shirye shiryen dawo da sauraron shari´ar tsohon shugaban kasar Liberia, wato Charles Taylor, daga Saliyo izuwa kasar Holland.
Da alama dai Mdd zata zartar da kudurin da zai ba da wannan damar ne a cikin wannan mako mai kamawa.
Kokarin daukar wannan mataki dai ya samo asali ne da bukatar yin hakan daga kotun kasa da kasa ta Mdd dake sauraron shari´ar a Saliyo.
Daukar wannan mataki kuwa daga bangaren wannan kotu nada nasaba ne da dalilai na tsaro kamar yadda suka shaidar.
Ya zuwa yanzu dai Mr Charles Taylor na fuskantar caje caje ne a kalla guda 17 dake da nasaba da miyagun laifuffuka na take hakkin bil adama , a lokacin yakin basasa da kasar ta Liberia ta fuskanta a shekarun 1991 izuwa 2002.