Charles Taylor ya ce komawar sa Liberia haɗari ga ƙasar.
March 21, 2006Tsofan shugaban ƙasar Liberia Charles Taylor, ya maida martini karo na farko, ga bukatar dassa ƙeyar sa, zuwa Liberia, domin fuskantar shari´a.
Charles Taylor, ya maida martanin ta hanyar mashawarcin sa, na ƙut da ƙut KIlari Anand Paul, da ya gana da shi, a jihar calabar tarayya Nigeria ,inda ya ya ke ci gaba da gudun hijira.
Kilari Anand Paul , ya bayana cewa, maida Chrles Taylor Liberia, ko kuma gurfanar da shi,kotun leffikan yaƙi, ko shaka babu, zai, hasadsa wani saban ruɗani, da yaƙe- yaƙe, a wannan ƙasa, ta la´akari da yadda yake samun goyan baya, daga jama´ar ƙasa, mussaman ɓangaren sojoji.
A satin da ya gabata, ita kanta shugabar ƙasar Liberia, Ellen Sirleaf Johson, ta bayana bukatar gurfanar da Charles Taylor gaban kotunan ƙasar Liberia.