Cheikh Anta Diop: Marubucin littattafan kimiyya
July 25, 2018Ya samu tallafin karatu inda ya je Faransa a shekarar 1946 har ma ya zabi darussa na kimiyya kafin daga bisani ya koma karanta falsafa da tarihi. Ya rubuta kundinsa na digiri kan yadda Afrika take kafin mulkin mallaka da kuma batun da ya danganci al'ada a kasashen Afirka bakar fata. Cheikh Anta Diop mutum ne dan kishin kasa kana ya yi fafutuka wajen ganin Afirka ta kasance tsintsiya madaurinki daya. Ya koma gida Senegal a shekarar 1960 inda ya mai da hankali wajen koyarwa da bincike kan harkokin siyasa har lokacin da ya rasu a shekarar 1986.
Abin da ya sa Cheikh Anta Diop yin fice
Cheikh Anta Diop kwararren marubuci ne, don ya yi rubuce-rubucen littattafai kan kimiyya da tarihin nahiyar Afirka.
· Da yake bayani game da alaka tsakanin harsunan Afirka, Cheick Diop ya ce yarensu na Wolof da kuma tsarin Masar na wancan lokacin ya nuna cewar Masar fa ta 'yan Afirka bakar fata ce.
· Cheikh Anta Diop na da digiri a ilimin hada sinadarai wato Chemistry da kuma abin da ya danganci harkar nukiliya. A shekarar 1966 ce ya girka dakin gudanar da bincike na farko a Afirka, wanda yanzu haka yake a jami'ar Senegal wadda aka sanya wa sunansa.
· Lokacin da yake dalibi ya yi fafutuka wajen ganin kasashen Afirka sun samu mulkin kai, daga baya kuma ya zama jigo wajen ganin an samu tsarin federaliyya a Afirka, har ma ya gabatar da haka a wani littafi mai suna The Economic and Cultural Foundations of a Federated State of Black Africa (1960, editor: présence africaine).
Wasu daga cikin fitattun kalaman Cheikh Anta Diop
"Yadda Masar take ga Afirka daidai yake da yadda Girka take ga Roma a yammacin duniya.”
"Samun cikakkiyar al'ada na taimakawa wajen baiwa mutane dama ta ba da gudunmawa wajen samun ci gaban al'umma.”
"Yana da kyau wanda ke fakewa da kimiyya su fahimci cewar lokacin yaudarar mutane da rinto kan harkoki na ilimi ya wuce. A bude wani sabon babi na tarihi kan batun harkokin ilimi tsakanin al'umma.”
Aiyukan Cheikh Anta Diop ba su da kokonto?
Lokacin da aka buga littafinsa na Negro Nations and Culture a shekarar 1954, Cheikh Anta Diop ya fuskanci caccaka daga masana ilimi da dama musamman da yake ya yi batu na wariyar launin fata da ya ce an gada daga turawan mulkin mallaka. Wasu daga cikin abokan aikinsa sun zarge shi da yin amfani da tsarin da ke haifar da cece-kuce. A shekarar 1974 ne masana tarihin Masar suka yabawa rubuce-rubucen da ya yi lokacin wani taro da aka yi. Tun daga wannan lokacin ne aka amince da su a matsayin gaskiyar da aka fito da ita a kimiyyance.
Karkashin shirin na musamman da DW kan tsara na Tushen Afirka bisa tallafi na gidauniyar Gerda Henkel.