China za ta aike da sojinta Sudan ta Kudu
December 22, 2014Talla
Kamfanin dillacin labarai na Xinhua da ke kasar ta China ya ce mahukuntan Beijing din za su aike da soji 700 ne. Daga watan Janairun da ke tafe ne dai za a fara aikewa da sojin kuma rahotanni daga Beijing din na cewar za a fara mutane 180 daga bisani cikin watan Maris da ke tafe a aike da sauran 520 din.
Sojin dai za su tafi ne da kayan yakin da suka hada da motoci masu sulke da jirage masu sarrafa kansu. Wannan dai shi ne karon farko China din ke aikewa da sojin da za su shiga fagen daga. Hakan kuwa na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar taryyar Turai ta EU ta bada sanarwar karin tallafi na sama da dala miliyan dubu biyu ga kasar ta Sudan ta Kudu.