1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cholera ta halaka mutane 65 a Nijar

September 27, 2018

Hukumomin lafiya sun tabbatar da cewar sama da mutum dubu biyu na fama da cutar amai da gudawa a jihar Maradi da ke makotaka da wasu jihohin Najeriya da ambaliyar ruwa ta shafa.

https://p.dw.com/p/35a2i
Krankenhaus in Niamey, Niger
Hoto: NigerInter.com

Bayan wani binciken da ma'aikatar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar, an tabbatar da mutuwar mutane 55 a farkon watan Satumban da muke ciki, bayan samu wasu daruruwan jama'a da cutar ta kama.

Kashi 22 cikin dari na mutane da ke fama da cutar cholera a Nijar sun fito ne daga jihohin Najeriya da ke makotaka da Jamhuriyar ta Nijar wadanda yawancin annobar ambaliya ta shafa.

Kungiyar Tarayyar Turai tare da hadin gwiwar gwamnatin Italiya sun ba da tallafi ga wadanda ke fama da cutar, yayin da gwamnatin Nijar ta dauki matakan dakile cutar tare da wayar da wa jama'a kai ta kafofin yada labarai.