Cholera ta hallaka mutane da dama a Juba
May 19, 2014Talla
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akalla mutane tara sun mutu sannan kimanin 138 na karbar magani a asibiti sakamakon barkewar annobar cutar amai da gudawa ko kuma Cholera a kasar Sudan ta Kudu. Hukumar ta WHO ta ce annobar na nuna alamun yin muni kuma yawan wadanda ke kamuwa da cutar ta Cholera ka iya karuwa. Yanzu haka dai hukumar da kuma sauran kungiyoyin agaji sun dukufa wajen tura magunguna yankin da abin ya shafa da ke kewayen Juba babban birnin kasar. Da ma dai kungiyoyin agaji sun yi gargadi game da wani bala'i ga dan Adam musamman na barazanar matsananciyar yunwa idan 'yan tawaye da dakarun gwamnati suka ci gaba da fada.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu