Ci gaba da barin wuta a Siriya
November 6, 2014Talla
Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya ce ta tabbara da hakan inda ta ce an kashe mayakan na Al-Nusra Front da ke da alaka da al-Qa'ida masu yawa a harin da jiragen yakin suka kai musu a shalkwatarsu da ke arewa maso gabshin Siriyan. Wanna dai shine karo na biyu da sojojin taron dangin karkashin jagorancin Amirka suka kai farmaki a kan wata kungiya da ba ta IS ba da ke yaki a Siriya. Kungiyar ta Al-Nusra Front dai na daya daga kungiyoyin 'yan tawaye da ke yakar gwamnatin Bashar Al-Assad na Siriyan sama da tsahon shekaru ukun da suka gabata.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman