Ci gaba da kwato iko daga kungiyar IS
February 24, 2017Talla
Dakarun kasar Iraki sun shiga wasu yankunan da ke yamma da birnin Mosul wani babban yanki da mayakan IS ke sheke ayarsu gabanin matsin lamba da suke fuskanta a halin yanzu. Bayanai sun ce an hango jiragen yakin kasar na lugudan wuta kan sansanonin mayakan IS a wani yanki na Syria, lamarin da wasu a Damascus suka kira hare-haren hadin guiwa ne tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.
A wasu jerin hare-haren neman kwato birnin Mosul daga 'yan jihadin na IS, a karon farko an ga manyan jiragen yakin Irakin na ta dannawa ta gabar yammacin kogin Jordan. Bayan kwato babban filin tashi da saukar jiragen birnin na Mosul a ranar Alhamis, rahotanni sun ce ana can ana ci gaba da barin wuta musamman a wurare da ke makwabtaka da wajen da ake kira Jaw Sag.