1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da rikici a Sudan ta Kudu

January 3, 2014

'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun fara ja da baya a dai dai lokacin da sojojin gwamnati ke ci gaba da kokarin sake kwace iko da garin Bor.

https://p.dw.com/p/1Aksb
Hoto: Samir Bol/AFP/Getty Images

Kakakin rundunar sojin kasar Philip Aguerm, ne ya sanar da hakan inda kuma ya nunar da cewa suna da wadatattun sojoji da za su yaki 'yan tawayen da suka mamaye garin na Bor, wanda iko da shi ya rinka zagaye tsakanin 'yan tawaye da sojojin gwamnati har karo uku tun bayan fara fadan kabilancin da ya rikide ya koma tamkar yakin basasa. Wanna dai na zuwa ne a yayin da ake kokarin sulhunta bangarorin biyu dake gaba da juna wato magoya bayan shugaban kasar mai ci yanzu Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa kuma babban abokin adawarsa Riek Machar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Tuni dai kasar Amirka ta bada umurnin kwashe sauran 'yan kasarta daga Juba babban birnin kasar ta Sudan ta Kudu sakamakon matsalar rashin tsaro da kuma tashin hankali da ke kara klazanta a jaririyar kasar da ta samu 'yancin kanta daga Sudan shekaru biyun da suka gabata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman