Ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Hamas da Isra'ila
August 8, 2014Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Masar din da ta tabbatar da wannan labarin ta ce bangarorin biyu sun amince kan abubuwa da dama inda ta nemi Isra'ila da Hamas su amince da wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku.
To sai dai a daura da wannan, kungiyar Hamas da dakarun Isra'ila sun ci gaba da kaiwa juna farmaki inda rahotanni ke cewar hakan ya yi sanadiyar rasuwar wani yaro dan shekara goma da kuma jikkata wasu sojin Isra'ila biyu.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Suleiman Babayo