Ci gaba da zanga-zanga a Senegal
February 1, 2012
A jamhuriyar Niger kawancan kungiyoyin fararan hula masu da'awar kare democrasiyya a cikin kasashen nahyar Afrika wato RODAD a takaice,ya kira taron manema labarai a birnin Yamai inda ya bayyana goyan bayansa ga kokowar da yan kasar Senegal su ke yi ta neman hanawa Abdoulaye Wade shugaban kasar mai ci a yanzu damar yin tazarce. Kungiyar ta RODAD wacce ta halarci taron gangamin kungiyoyin fararan hula na nuna adawa da takarar Abdoulaye Wade,ta kira wannan taron ne domin bayyanawa yan kasar ta niger halin da ake ciki a kasar Senegal da kuma fargabar da ta ke yi a game da tasirin da wannan rikici ka iya yi ga
demokradiyyar sauran kasashen nahiyar ta Afirka.
Kungiyar ta RODAD wacce ta ke daya daga cikin jerin kungiyoyin fararan hula na kasar Niger da ke da'awar kare tafarkin demokrasiyya a kasashen na nahiyar Afirka ta kira wannan taro ne jim kadan bayan da wata tawagar mambobinta ta dawo daga kasar Senegal,inda ta halarci babban taron gangamin kaddamar da shirin yaki da yinkurin tazarcen Abdoulaye Wade shugaban kasar ta Senegal da kungiyoyin fararan hular kasar Senegal su ka dukufa. Mallam Lawal Sallau Tsayyabu, shugaban kungiyar ta RODAD ya yi karin bayani game da dalillansu na zuwa kai goyan baya ga yan kasar ta Senegal masu adawa da tazarcen Abdoulaye Wade.
"Da Niger ta shiga rikici kun ga yan uwammu na kasashen Afirka da suka hallara a nan Niger domin su kama mana da kokowar da mu ke da tazarce dan a dawo bisa hanya ta democrasiyya. To yau gareka gobe ga dan uwanka. Yau ga shi ta faru a kasar Senegal, wadda kasa ce da nan da shekara hamsin tun bayan samun yancin kai ba ta taba samu wani rikici ba da har ya kai ga juyin milki;kuma kasa ce wadda ake kallonta a matsayin wani madubi cikin kasashen Afirka a fannin democradiyya. To yau kasar ta shiga wani rikici tun da Wade ya zo yana so ya karkatar da akalar iko,yan senegal sun ce iko ba gado ba ne;to shi ya sa mu ka je kasar Cote d'Ivoire domin in yi taro na neman Wade ya sabka daga milki.
Kungiyar ta RODAD ta bayyana cewa nauyi ya rataya ga duk mai kishin demokrasiyya tashi shiga wannan kokowa domin kuwa a yau ta tabbata cewa shugaban kasar Senegal din wanda aka jima ana yi masa kallon dattijo,shine uban duk wani shiri na tazarce da ake fuskanta a kasashen Afrika.
"Wade shine gimshikin tazarce a cikin kasashen nahiyar Afirka duk wani wanda ya so ya yi tazarce har da miyan Wade a ciki. Ko Obasanjo da ya so ya yi tazarce a Najeriya akwai hannun Wade a ciki dan saboda shi Wade da ya yi ziyarar kasashe na Larabawa da ya dawo, sai cewa ya yi shi ya gane da jamhuriya aikin banza ne, abun da ya cancanci kasashen Afirka shine mulki na gargajiya. Har ma irin salon da Tandja yayi, kamar dai Wade ne yazo nan Niger ya koya masa yadda zai yi."
Kungiyar ta RODAD ta kuma bayyana damuwarta dangane da yanda ake samun sabanin ra'ayi tsakanin kasashen duniya dangane da wannan batu na kasar Senegal.Kasashen duniya hankalinsu ya rabu biyu: akwai wadanda su ka ce a bi
abinda doka ta ce, akwai wadanda su ka ce a yi amfani abin da mutane ke so. Kungiyar CEDEAO ko kuma ECOWAS ta ce a gami da yan adawa ya kamata a sasanta, amma su kasashen turai so su ke a bi hanyar abin da doka tace. Abin da doka ta ce shi kenan To menene ake so a aiwatar a tafarkin democradiya a kasar ta Senegal. Ko shin ana son samun irin abin da ya faru ne a Masar ko a Libya ko kuma kasar Tunisia.
Daga karshe dai kungiyar ta RODAD ta yi gargadin cewa idan dai har yan Afirka su ka zura ido tazarcen Aboulaye Wade ta yi nasara to ba shakka hakan zai kasance wata babbar nasara da za ta bayar da kwarin gwiwa ga sauran
shugabannin kasashen Afirka masu irin wannan nufi.
Mawallafi: Gazali Abdou Tassawa
Edita: Umaru Aliyu