Masu goyon bayan sojojin Sudan na zanga-zanga
October 18, 2021Talla
An sake samun mutane da dama da ke goyon bayan sojojin Sudan da suka yi zanga-zanga a birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar inda suke neman ganin Firaminista Abdalla Hamdok ya ajiye aiki.
Shi dai Firaminista Hamdok ya shaida wa majalisar zartaswar kasar cewa gwamnatin wucin gadin tana fuskantar rikici mafi hadari tun bayan da masu zanga-zanga suka kawo karshen gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir.
Ita dai gwamnatin wucin gadi ta Sudan tana kunshe da sojoji da fararen hula inda aka tsara za ta gudanar da zabuka zuwa shekara ta 2023.