1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban shari'ar Charles Taylor

August 5, 2010

Yau, Naomi Campbell ta bayyana a gaban kotu bisa yaƙin basasan Saliyo

https://p.dw.com/p/Od3t
Charles Taylor, ta hagu da Naomi Campbell, ta damaHoto: DPA

A yau ne aka ci gaba da sauraron shari'ar tsohon shugaban Laberiya, Charles Taylor a kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta musamman akan yaƙin basasan Saliyo, da ke a birnin the Hague na ƙasar Holland, bisa laifin taimaka wa yaƙin basasan, inda fitacciyar sarauniyar kyau wajen gwada ado ta ƙasar Birtaniya, Naomi Campbell ta bayyana a matsayin 'yar sheda.

"Mun yi imanin cewa akwai bayanai masu muhimmaci da za mu samu daga Naomi Campbell da kuma sauran shedu biyu da muka kira, akan zargin da ake yi wa Charles Taylor na mallakar damonti da aka kwasa a matsayin ganima a Saliyo."

Jawabin da Brenda Hollis jami'ar shigar da ƙara a kotun ta musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kenan, kafin fara sauraron shari'ar a birnin the Hague na ƙasar Holland.

Sierra Leone zu Beginn des Taylor-Prozesses
Wasu da aka datse wa gaɓoɓi a yaƙin basasan Saliyo.Hoto: picture-alliance/dpa

Tsohon shugaban na Laberiya dai ana tuhumarsa ne da laifin rura wutar yaƙin basasa da aka shafe shekaru 11 ana gwabzawa a ƙasar Saliyo, da kuɗin da ya samu daga haramtaccen fataucin damonti da aka kwasa a matsayin ganima yayin yaƙin. Lefukan da kotun ke tuhumar Charles Taylor akansu, sun haɗa ne da aikata kisan kai, da tilasta wa ƙananan yara shiga akin soja tare da daddatse gaɓoɓin 'yan adawa. A dai ƙoƙarin da kotun ke yi na neman shedar da ke tabbatar da wannan zargi da ake yi wa tsohon shugaban na Laberiya ne, ya sa aka nemi Naomi Campbell da ta bayyana a gaban kotun domin yin bayani dalla- dalla game da rahotannin da ke nuni da cewa tsohon shugaban na Laberiya ya ba ta kyautar damonti yayin ganawar da ta yi da shi a wani buki da tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela ya shirya domin yin karo-karon kuɗin tallafa wa marasa galihu. Da take ba da bahasi game da wannan zargi, Naomi Campbell ta ce ta amshi wannan kyautar ne daga hannun wasu mutane biyu da suka ƙwanƙwasa ƙofar masaukinta. Naomi ta ƙara da cewa ita kanta ba ta zaci damonti ne ke ƙunshe cikin 'yar jakar da mutanen biyu suka miƙa mata ba, kuma ba ta san ko wa nene ya aiko su ba. Ga dai irin tambayoyin da Brenda Hollis ta yi wa Campbell da kuma amsoshin da ita Campbell ta bayar

Niederlande Kriegsverbrechertribunal Den Haag Naomi Campbell
Naomi Campbell akan babban allon telebijan yayin shari'ar ta yau.Hoto: AP

Campbell: Da suka miƙa mini ƙunshin na ajiye shi a gefen gado na koma barci."

Hollis. Kenan a wannan lokaci ba ki ma duba domin ki gan abin da ke ciki ba?

Campbell: "Sai da gari ya waye ne na buɗe ƙunshin."

Hollis: "Da suka ta da ke daga barci kin tambaye su abin da ke ƙunshe?"

Capblell: " A' a kawai karɓa nayi na yi musu godiya."

Hollis: "Sun nuna miki dalilin da ya sa suka baki wannan ƙunshi?"

Campbell: "Babu wani bayani da suka yi mani, ko da baki ko a rubuce. Wasu 'yan ƙananan duwatsu ne masu datti."

Hollis: "Daga bisani me kika yi da waɗannan ƙananan duwatsu masu datti?"

Campbell ta ba da amsa tana mai cewa ta sauka da su ne zuwa ƙasa a lokacin da suke shirin karya kumallo, kana ta ba da su a matsayin sadaka domin taimaka wa marasa galihu.

Naomi Campbell, wadda da farko ta musunta zargin cewa ta amshi kyautar damonti daga Cahrles Taylor dai, na ɗaya daga cikin 'yan sheda 91 da aka nema da su ba da bahasin game da wannan shari'a da ake wa Charles Taylor, da har yanzu kotun ba ta tabbatar da gaskiyar cewa yana da hannu a yaƙin basasan da aka shafe shekaru 11 ana yi ƙasar ta Saliyo ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal