Faransa: Ci gaban shari'ar Nicolas Sarkozy
January 7, 2025Sai dai wannan shari'a da ake sa ran za ta dauki watanni da dama tana gudana tana shan fassara iri dabam-dabam a yankin Sahel, domin wasu jami'ai na danganta faduwar gwamnatin Muammar Gaddafi da zama tushen tabarbarewar harkokin tsaro a yankin. Kotun dai, na tuhumar Nicolas Sarkozy da wasu mukarrabansa 12 da laifukan da suka hada da cin-hanci da karbar rashawa da almundahana da dukiyar kasa da neman kudin yakin neman zabe ba bisa ka'ida ba da kuma hada kai wajen aikata laifuka. Tsohon shugaban na Faransa na iya fuskantar zaman gidan yari na shekaru 10 da tarar Euro dubu 375 idan aka same shi da wadannan lafuka da soke wasu hakkokinsa na tsawon shekaru biyar, lamarin da zai hana shi tsayawa takara har zuwa wani lokaci. Da ma dai wata kotu ta fara kama Sarkozy da laifin samun kudin yakin neman zabe ba bisa ka'ida ba, hukuncin da kotun daukaka kara ta tabbatar.
Hasali ma dai, wannan shari'ar na da alaka da kashe kudin da ya zarta kima a lokacin yakin neman zabensa na 2012, sai dai tsohon shugaban na Faransa ya daukaka kara zuwa kotun gaba. Amma dai, wasu jami'an gwamnatocin Afirka na alakanta rikicin da Libiya ta samu kanta a ciki a zamanin mulkin Sarkozy a Faransan da ayyukan ta'addanci da ake fuskanta a yankin Sahel. Ko da ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop na daga cikin wadanda ke wannan ikirarin. Irin wannan ra'ayi mai bincike a cibiyar nazarin tsaro (ISS) da ke Dakar Hassan Koné yake da shi, inda ya ce hambarar da gwamnatin Gaddafi a watan Maris din shekara ta 2011 da Sarkozy ya yi bayan da ta su ta hadasu, shi ne ya kara haddasa tabarbarewar harkokin tsaro a yankin baki daya. Kafin faduwar gwamnatinsa, Gaddafi ya samu karbuwa sosai a karshen shekara ta 2007 a birnin Paris daga hannun Sarkozy da shi ne zababben shugaban kasa a wancan lokacin. Amma daga bisani, dangantakarsu ta tabarbare.
Saboda haka ne yayin da guguwar neman sauyi ta kada a Libiya, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kuduri mai lamba 1973 a ranar 17 ga Maris na 2011 da Faransa da Birtaniya suka gabatar. Wannan ya ba da izinin yin amfani da karfi, domin kare fararen hula da kuma kawo karshen tashin hankali. Sai dai Gaddafi ya mutu a watan Oktoba na 2011, inda abokan adawa suka yi amfani da wannan dama wajen ganin bayansa. Wai shin, faduwar gwamnatin Gaddafi na da alaka da abin da ke faruwa yanzu haka a fuskar tsaro a yankin Sahel? Kwararriyar mai bincike daga kungiyar International Crisis Group Claudia Gazzani ta ce tabbas akwai alaka a wani bangare, amma ba gaba daya ba. Sai dai kwararriyar a harkokin kasar Libiya, ta yi nuni da cewa akwai wasu dalilai na cikin gida da ke haifar da matsaloli a kasashe kamar Mali da Nijar da Burkina Faso. Shi ma Aly Tounkara na cibiyar tsaro da nazarin dabaru a yankin Sahel (C4S) na da wannan ra'ayi, inda ya ce rufe ido kan matsalolin da faduwar gwamnatin Gaddafi ta haifar ba abu ne da zai yiwu ba. Dalili kuwa shi ne, kungiyoyin 'yan ta'adda sun samu nasarar kwatar makamai a lokacin da aka kai hare-hare a yankin Sahel.