CIA ta bankado umarnin kashe Jamal Khashoggi
November 17, 2018Jami'an hukumar Leken Asirin Amirka sun yanke cewar Yarima Muhammad bin Salman na kasar Saudiyya ne ya bada umarnin a kashe 'dan Jaridar nan Jamal Kashoggi.
Sai dai babu tabbas ko jakadan Saudiyya a Turkiyya na da masaniya game da shirin aikata kisan kai a karamin ofishin Jakadancin Saudiyan dake Istanbul cikin sakamkon binciken da suka gudanar sai dai gwamnatin Saudiyya ta yi watsi da wannan batu.
A wani sabon labarin kuma Hukumar ta bankado wata hira tsakanin marigayi Kashoggi da Khalid bin Salman Jakadan Saudiyya a Amirka a wayar tarho inda Jakadan ya ke ba Kashoggi tabbacin tsaron lafiyar sa idan ya je karbar takardun neman sabon auren da zai yi a karamin Ofishin jakadancin Saudiyyan dake Istanbul .
Masu rajin kare hakkin dan Adam dai na ci gaba da yin Allah wadai da kokarin tsame Yarima Muhammad bin Salman daga zargin kisan dan Jaridar Jamal Kashoggi