1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin mata da karuwar kabilanci a Sudan ta Kudu

Salissou Boukari
December 14, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta soki irin cin zarafin da ake yi wa mata da kuma batun kabilanci a Sudan ta Kudu, inda ta nemi da a samar da sojoji 4000 da za su samar da tsaro a dukannan sassan kasar.

https://p.dw.com/p/2UG66
Schweiz Genf Choi Kyong-lim (L), Zeid Ra'ad Al Hussein, UN Human Rights Council
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Campardo

Wannan kira ya fito a wannan Laraba yayin buda zaman taro na musamman kan kasar ta Sudan ta Kudu da aka kira bisa tambayar kasashe 48 bisa jagorancin Amirka domin duba wadannan batutuwa. A cikin wani jawabi da ya yi lokacin soma mahawarar, babban Sakataran Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin kare hakin dan Adam Zeid Ra'ad Al-Hussein, ya ce tattalin arzikin kasar ta Sudan ta Kudu ya tabarbare baki dayansa sakamakon yakin da kasar ke fama da shi na tsawon shekaru uku.

Akalla mutane fiye da miliyan hudu ne 'yan kasar ta Sudan ta Kudu suka rasa komai nasu, inda a halin yanzu suke fuskantar babban kalubale na rishin abinci a cewar Majalisar Dinkin Duniya. Ita kuma daga nata bangare shugabar hukumar kare hakin dan Adam ta Sudan ta Kudu Yasmin Sooka, ta soki matakin da aka dauka a wasu yankunan kasar na kisan kare dangi kan wata kabila a kasar.