Cinkoson gidajen kaso na kasar Faransa
January 19, 2018Talla
Wannan kira na daga cikin shawarwari har guda 300 da kwamitin ya bai wa kasar ta Faransa na ganin ta inganta tsarin nata na kula da gidajen kasonta da suke fama da tarin matsaloli na cinkoson jama'a.
Wannan mataki na daga cikin tsarin kwamitin, inda duk bayan shekaru hudu ake zabar wata kasa domin duba tsarinta na kare hakin bil-Adama.
Kasashen kuma sun yi kira ga kasar ta Faransa da ta tabbatar cewa dokokinta da take amfani da su na yaki da ta'addanci, dokoki ne da suka dace da dokokin kasa da kasa har ma abin da ya shafi 'yan gudun hijira masu karancin shekaru.