Mutane 56,000 suka kamu da Corona kawo yanzu
March 26, 2020Talla
Wannan kuma na faruwa ne duk da matakan jingine abubuwan shakatawa da mahukumta suka dauka a kwanaki 12 da suka wuce.
Kamfanin dillancin labarai na Jamus, DPA, ya ce kawo yanzu kasar Spain ta samu karin mutane sabbin kamu da suka kai akalla 8,500, abin da ya kara fadada yawan mutanen da suka kamu a kasar zuwa 56,000. Akalla mutane 4,000 Coronavirus ta kashe a Spain kawo yanzu, galibi a birnin Madrid inda cutar tafi kamari.
A kasar Italiya kuwa wace ke zama dandazon masu da Coronavirus a nahiyar Turai, rahotanni sun ce kawo yanzu mutane sama da 74,00 suka kamu da wannan ciwo.