1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai: Matakin Trump kan Coronavirus a Turai

Ramatu Garba Baba ZMA
March 12, 2020

Shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da dakatar da dukkan wasu tafiye-tafiye daga kasashen Turai zuwa Amirka in banda kasar Birtaniya na tsawon kwanaki 30.

https://p.dw.com/p/3ZILf
US-Präsident Trump spricht über die Reaktion der USA auf die COVID-19-Coronavirus-Pandemie
Hoto: Reuters/D. Mills

 

Sanarwar na zuwa ne jim kadan da sanarwar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi na ayyana Coronavirus a matsayin annobar da ta shafi duniya baki. Sai dai matakin Amurkan ya zo wa da dama da mamaki musanman nahiyar Turan da lamarin ya shafa.

Tuni kungiyar ta mayar da martanai inda ta nuna bacin rai kan matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka ba tare da ya soma tuntubarsu ba. Kuma  Kakakin hukumar tarayyar ta Turai Eric Mamer ya yi karin bayani:

 "Coronavirus annoba ce da ta shafi duniya baki daya don haka taron dangi ya dace a mata, maimakon a ce kasa guda ta ware kanta da sunan son kare kanta daga wannan annoba. Saboda haka da babban murya  Kungiyar Tarayyar Turai bata amince da matakin da Amurka ta dauka ba na hana 'yan kasashen nahiyar Turan izinin shiga kasar ba tare da an tuntubi Kungiyar ba tukun na musanman ganin yadda muka dage na hana yaduwar cutar dama dakileta baki daya''.

Russland Moskau Kontrollen wegen Coronavirus am Flughafen Scheremetjewo
Hoto: picture-alliance/TASS/Moscow Healthcare Department

Shakka babu matafiya da dama sun sami kansu cikin tsaka mai wuya, musanman wadanda suka riga suka siyi tikiti suke kuma shirin zuwa kasar da dama ke kokarin hana yaduwar cutar ta Coronavirus da ya zargi tarayyar Turan da kin daukar kwararran matakan hana yaduwarta, wannan Bajamushen Christian Juenemann ya diga ayar tamabaya kan tasirin matakain na Shugaba Trump:

''Yanzu abu ne mai wuya a iya sanin ko kwalliya zata biya kudin sabulu a wannan matakin da ta dauka na son kare kanta daga wannan annobar ta Coronavirus, baki daya bana ganin matakin zai taimaka ma kasar ko tattalin arzikinta‘‘

Ra'ayi dai riga don kuwa wannan matafiyar mai suna Agatha Czerwinska, ta ce ba ta ga laifin haramcin ba akwai yiyuwar matakin ya cimma burin shugaban amma kuma mai ma na damuwa, ai kamata ya yi a ci gaba da daukar matakaki na tsafta da na wanke hannu da sauransu amma yanzu mun zura idanu muga yadda zata kaya, bana jin akwai wani abin fargaba".