Trump ya yi gaban kanshi a kan Corona
March 12, 2020Talla
A cikin wata sanarwa da suka fitar, Shugabannin kungiyar tarayyar Turai sun ce ba su ji dadin hana wasu 'yan kasashen nahiyar zuwa Amirka da Shugaba Donald Trump ya yi ba. Shugabannin sun ce Trump ya yi gaba-gadi wurin daukar wannan mataki ba tare da tuntubarsu ba. Shugabar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta sanar a cikin wata sanarwa cewa ''cutar Corona matsala ce da ta shafi kowane bangare na duniya, ba kuma ta takaita ga wata nahiya kadai ba. A don haka ana bukatar hadin-kai da aiki tare wurin murkushe cutar a maimakon wani ya yi gaban-kanshi''.