COVID-19: Jamus ta bukaci hadin kan duniya
April 11, 2020Talla
Shugaban na Jmaus, Frank-Walter Steinmeier,na fadin hakan ne a jawabinsa na farko a hukumance bayan wanda ya yi lokacin Kirsimeti, inda ya jaddada bukatar taimakekeniya tsakanin jama'a.
Ya yi bayanin cewa Jamus ba za ta iya fita daga kangin wannan annoba ba, har sai ta taimaka wa makwabtanta da ke cikin ja'ibar cutar, a saboda hakan ne ya nuna muhimmancin hadin kai a tsakanin kasashen duniya.
Da yake martani kan wadanda ke cewa duniya na yanayi na yaki kuwa, Steinmeier, ya musanta hakan, inda ya ce babu kasar da ke fito-na-fito da wata a wannan lamarin, kawai dai gwaji ne ga imaninmu.